Kotu a Masar ta yanke hukuncin za a sallami gwamman mambobin Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da aka tsare a garin Iskandariyya na arewacin kasar.
Wani mambon 'Yan Uwa Musulmi da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa, ba a kammala sakin mutanen gaba daya ba, amma an nuna alamun za a sallame su saboda wata shari'ar ta daban, a nan gaba kadan za a tabbatar da halin da ake ciki.
Jami'an gwamnatin Masar ba su ce komai ba game da batun.
A ranar Talatar makon da ya gabata gwamnatin Masar ta sanar da cewa, sakamakon zuwan azumin Ramadhan an yi wa fursunoni dubu 1,686 afuwa tare da sallamar su.
A shekarar 2013 ne bayan juyin mulki a Masar gwamnai ta aiyana kungiyar 'Yan Uwa Musulmi a matsayin ta ta'adda tare da haramta aiyukanta.