Ana samun ci gaba wajan dawo da kasashen AES cikin ECOWAS - Faye

Ana samun ci gaba wajan dawo da kasashen AES cikin ECOWAS - Faye

A watan jainairun wannan shekarar ne kasashen 3 suka sanar da ficewa daga kungiyar tarayyar kasashen yammacin afrika, inda suka kulla kawance tsakanin su, tare  da zargin kasar da kin taimaka musu wajen yaki da yan ta’adda a yankin.

A yayin da wadannan kasashe ke Shirin cika shekara 1 da ficewarsu daga kungiya a watan Janairun 2025,akwai yiwuwar su kulla yarjejeniya da kasar Russia,sai dai shugaba faye a yayin taron sulhu a birnin Doha dake kasar Qatar yace, yana iya kokarin sa na ganin cewar ya shawo kan lamarin.

A watan yuli ne kungiyar ECOWAS ta nada faye a matsayin mai shiga tsakani domin rinjayar kasashen su koma cikin ECOWAS

Kasashen  Burkina faso, mali da Nijar na fama da matsalar rashin tsaro a yankin daya samo asali daga mali a shekarar 2012 kuma ya bazu zuwa kasashen a shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)