An fara gudanar da bikin ne a ranar 26 ga watan Agustan 2015, wanda Hausawa a ƙasahen Najeriya, Nijar, Kamaru, Chadi da sauran ƙasashen yammacin Afrika suka fi gudanarwa.
Harshen Hausa dai shine harshe mafi saurin yaɗuwa a sassan Afrika wanda masana ke alaƙanta hakan da yawo da kuma harkokin kasuwanci da Bahaushe yayi ƙaurin suna akai.
Bayanai sun nuna cewa zuwa yanzu harshen Hausa ko kuma masu amfani da shi sun zarce Nahiyar Afrika, inda suka tsallaka zuwa Amurka da Turai, gatan da babu wani yare a Afrika da ya sami makamancin sa.
Bisa al’ada dai, a irin wannan rana akan gudanar da bubukuwa da kuma taruka don tattaunawa da juna a ko ina a duniya, don lalubo matsalolin da harshen ke fuskanta da kuma yunƙurin shawo kan matsalar.
Hausawa sun yi bankwana da wasu sunayensu na gargajiya. PinterestCikin matsalolin da harshen ke fuskanta akwai yadda wasu tsaffin kalmomi ke ɓata sakamakon yanayi na chakuɗuwar malaman Bahaushe da Larabawa da kuma Turawa, to amma wasu masana na ganin hakan ba matsala bane illa ma yana ƙara kambama yaren da bashi damar ƙirƙirar sabbin kalmomin da ake Hausantar da su.
A irin wannan rana ne za’a ga yadda ƙarfin Hausa yake ta yadda matasa da kuma sauran masu sha’awa ke ruwan karin magana, habaici, ko kuma Zambo duk dai don bikin ranar.
A wannan rana ma dai jami’o’i musamman a Najeriya da kuma Ghana sun shirya taruka na musamman don tattaunawa kan maƙalu daban-daban da suka shafi yaren Hausa, al’adu da kuma yanayin rayuwar Bahaushe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI