Ana fargabar yadda wasu kasashen Afirka ba za su iya samun riga-kafin Corona ba

Ana fargabar yadda wasu kasashen Afirka ba za su iya samun riga-kafin Corona ba

Kasashen Afirka matalauta na fargabar yadda ba za su iya samun alluran riga-kafin cutar Corona (Covid-19) ba kamar yadda ya kamata.

Daraktan Hukumar Yaki da Cututtuka ta Afirka (Africa CDC) Dr. John Nkengasong ya bayyana cewar, nan da watanni 3 na 2 na shekarar 2021 za a iya fara yin allurar riga-kafin Corona a Afirka, kuma zai zama abu mai hatsari idan kasashen da suka ci gaba suka yi allurar riga-kafi amma suka hana 'yan kasashen da ba su da ita izinin shiga kasashensu.

Ya ce "A lokacin da cutar Corona ta bulla, mun ga yadda aka kyale Afirka ita kadai. Akwai bukatar allurar guda biliyan 1,5 domin amfani da ita a nahiyar Afirka."

Daraktar Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta Afirka Dr. Matshidiso Moeti ta bayyana cewar, kasashen nahiyar da dama na gwagwarmayar yadda za su sayi alluran riga-kafin Corona.

Ta ce "Kasashen Afirka na da fargaba, kar kasashe masu kudi su hana Afirka samu sakamakon yadda tuni suka bayyana aniyarsu na sayen alluran daga hannun kamfanunnuka."

Ta kuma  ce, wasu kasashen Afirka da dama sun kasance tare da kayan taimako na abubuwan rufe fuska da aka kai musu kawai wanda ba su ishe su ba, sannan wasun su sun wahala wajen sayen maganin cutar.


News Source:   ()