Kafofin yaɗa labarai a Senegal sun ce sa’o’i ƙalilan bayan da jirgin ya bar gaɓar teku a ƙasar daga garin Mbour ne ya nutse a cikin ruwan bayan tafiyar kilomita 4 kaɗai a kan teku, ko da ya ke an yi nasarar ceto mutane 4 da ransu.
Rahotanni sun ce ƴan ciranin waɗanda suka kama hanyar isa Turai ne a cikin wani jirgin kwale-kwale na katako irin na masunta da ake aikin kamun kifi da shi, lamarin da ya kai ga nutsewarsa saboda nauyin da suka yi masa.
Kawo yanzu gawarwakin mutane 6 aka tsamo yayinda gawarwakin ƴan cirani fiye da 100 suka yi ɓatan dabo a cikin ruwa.
Rundunar Sojin ruwan Senegal wadda dakarunta ne suka gano haɗarin jirgin tare da nasarar ceto mutum 4 da ransu da kuma tsamo gawarwakin mutum 6, ta ce yanzu haka ta na kan aikin lalube don tsamo gawarwakin da suka nutse a ruwan da kuma yiwuwar ceto waɗanda ke da sauran lumfashi.
Tun a yammacin Lahadin da ta gabata ne haɗarin ya faru a wani yanayi da alƙaluma ke nuna ƙaruwar ƴan ciranin da ke bin wannan hanya zuwa tsibirin Canary don samun rayuwa mai inganci a Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI