A kasar Mali, gwamnatin soji da ta yi juyin mulki ta janye wata doka da ta samar wadda ta ba wa mataimakin shugaban kasar ikon karbar wakilcin Shugabancin kasa.
Bayan da aka sanar da Firaminista da Mataimakin Shugaban Kasa a Mali ne aka sa ran Kungiyar ECOWAS za ta janye takunkuman da aka saka wa kasar, kuma sai ga shi sojojin sun sake daukar wani sabon mataki.
Sabon matakin da aka dauka kuma aka buga a jaridar gwamnati ya bayyana cewar, Mataimakin Shugaban Kasa na da alhakin kula da Maikatar Tsaro ne kawai, inda aka cire sashe na 7 na tsohuwar dokar da ta ba shi ikon karbar kujerar Shugaban Kasa a matsayin wakilci.
ECOWAS ce ta kayar da martani na nuna rashin amincewa da damar da aka ba wa Mataimakin Shugaban Kasa kuma sojan da ya jagoranci juyin mulki Assimi Goita.