Mutane shida sun mutu a zanga-zangar neman dawo da mulkin farar hula da aka gudanar a Chadi.
Kakakin Babban Kwamishina na Kare Hakkin Dan-Adam na Majalisar Dinkin Duniya (OHCHR), Marta Hurtado, a cikin wata rubutacciyar sanarwa, ta bayyana cewa an kashe mutane 6 kuma an tsare fiye da mutane 700 a zanga-zangar da aka gudanar a ranar 27 ga Afrilu a Chadi da ake kalubalantar gwamnatin wuccin gadi.
Hurtado ta jaddada cewa ya kamata a saki wadanda aka kaman cikin gaggawa, kuma ta bayyana cewa ba za a yarda da jami'an tsaro su yi amfani da harsasai na gaske da murgunawa al'umma a yayin zanga-zangar ba.
Da take neman hukumomi da su umarci jami'an tsaro da kada su yi amfani da karfi a kan masu zanga-zangar da ke amfani da 'yancinsu na faɗin albarkacin bakinsu, Hurtado ta yi kira ga gwamnatin Chadi da ta kiyaye haƙƙin ɗan adam, tana mai tunatar da su da cewa hukumonin kare hakkin dan adam na kasa da kasa na sanya ido akan abubuwan da ke faruwa a kasar.
Hurtado ta nemi gwamnatin Chadi da ta kaddamar da bincike don yin karin haske kan tashe-tashen hankula da take hakkin bil adama a kasar.
A cikin rubutacciyar sanarwar da ta fitar, kungiyar Tarayyar Afirka ta sanar da cewa ta kaddamar da wata tawagar bincike a kasar don tallafa wa binciken rikicin siyasar Chadi da kuma mutuwar tsohon shugaban kasar Idris Deby Itno.
A cikin sanarwar, an bayyana cewa, tawagar za ta kuma goyi bayan dawo da tsarin mulkin farar hula a kasar