Ana ci gaba da neman fursunonin da suka tsere daga gidan kurkuku a Najeriya

Sakamakon harin 'yan bindiga, daruruwan fursunoni sun tsere daga gidan kurkukun Owerri Babban Birnin jihar Imo da ke kudu maso-gabashin Najeriya.

Labaran da jaridun Najeriya suka fitar sun ce, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba ne suka kai hari kan gidan kurkuku na Owerri wanda hakan ya baiwa daruruwan fursunoni damar guduwa.

An bude wuta kan gidan yarin tare da kona motoci da yawa.

'Yan a waren Biafra daake kira IPOB na kai irin wadannan hare-hare a Najeriya.

'Yan a waren IPOB da Najeriya ta aiyana a matsayin 'yan ta'adda na son kafa kasar Biafra.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya la'anci harin da ya kira na ta'addanci, ya kuma umar-ci jami'an tsaro da su kamo maharan.

 


News Source:   ()