Ana ci gaba da laluben waɗanda suka suka a haɗarin jirgin ruwa a DR Congo

Ana ci gaba da laluben waɗanda suka suka a haɗarin jirgin ruwa a DR Congo

Kwale kwalen da aka maƙare da fasinjoji fiye da kima ya kife ne a wani kogi da ke tsakiyar Jamhuriyar Congono.

Bayanan Jami’ai da wasu mazauna yankin da haɗarin ya faru sun ce akwai mata da ƙananan yara a cikin mutanen 25 da suka rasa rayukansu

Kwale-kwalen na dauke ne da fasinjoji sama da 100, wanda ya tashi daga yankin Inongo na arewa maso gabashin babban birnin kasar Kinshasa, a ranar Talata, yana kuma tsaka ta ratsa kogin Fimi ne a lokacin da ya nutse.

Hatsarin na ranar Talata shi ne na hudu da ya auku a cikin wannan shekarar a lardin Maï-Ndombe, yankin da koguna ke kewaye da shi.

Aƙalla mutane 78 suka nutse a cikin watan Oktoba lokacin da wani kwale-kwale ya nutse a gabashin ƙasar, yayin da a watan Yuni mutane 80 suka rasa rayukansu a wani hatsarin haɗarin jirgin ruwan a kusa da Kinshasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)