Ana ci gaba da kula da wadanda wata rikitacciyar cuta ta kama a Kano

Ana ci gaba da kula da wadanda wata rikitacciyar cuta ta kama a Kano

Mutum 1 ya rasa ransa yayinda aka kwantar da wasu 56 a asibiti sakamakon kamuwa da wata rikitacciyar cuta da ba a gano wacce iri ba ce a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Mahukuntan jihar sun bayyana cewa, ana ci gaba da gudanar da binciken gano musabbabin mutuwar mutum gudan, kuma wasu daga cikin wadanda aka kai asibiti suna amai da fitsarin jini.

A shekarar da ta gabata ma wata rikitacciyar cuta ta yi ajalin sama da mutane dubu guda a Kano.

 

 


News Source:   ()