Kalaman na Ramaphosa na zuwa ne a dai dai lokacin da kiraye-kiraye daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da kuma ɗaiɗaikun mutane ke ci gaba da tsananta, wajen ganin mahaƙan sun fito daga ramuka lafiya dai dai lokacin da ake fargabar mutuwar da dama daga cikinsu.
Fiye da masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba dubu guda ne suka miƙa kansu ga ƴan sandan Afrika ta kudu cikin makon jiya kaɗai, bayan da ƴan sandan suka kange duk wata hanyar shigar da abinci da ruwan sha ga ramukan ƙarƙashin ƙasa da mahaƙan ke aikin haƙar zinare a cikinsu.
Duk da yawan wannan adadi da suka miƙa wuya, ƴan sandan Afrika ta kudu sun yi amannar cewa akwai wasu ɗaruruwa ko kuma dubunnai da ke ƙarƙashin ƙasa dai dai lokacin da bayanai ke cewa yunwa na ci gaba da galabaitar da su, saboda rashin abinci da ruwansha.
A wani jawabi da shugaba Cyril Ramaphosa ya gabatar da safiyar yau Litinin shugaban ya ɓukatar yin taka-tsan-tsan da lafiyar mahaƙan waɗanda suka killacewa kansu yasassun mahaƙun yankin arewa maso yammacin ƙasar da aka daina amfani da su tsawon lokaci a koƙarin na laluben ɓirɓishin zinaren da ya rage.
A cewar shugaba Ramphosa, halin da ake ciki ka iya juyewa zuwa rikici inda ya roƙi ƴan sandan kan su kula da haƙƙin ɗan adam wajen fitar da mutanen daga ramukan cikin salama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI