A nahiyar Afirka an zubar da alluran riga-kafin cutar Corona har guda dubu 450.
Daraktan Samar da Garkuwar Jiki na Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) a Afirka Dr. Richard Mihigo ya shaida cewa, an zubar da alluran a kasashe 9 saboda kusantowar ranar karshe don amfani fa su.
Mahido ya ce, an zubar da allurai dubu 450 kuma hakan ta faru sabida kai kasashen a makare inda aka gaza yin amfani da su da wuri-wuri.
Kasashen da aka lalata alluran su ne; Gambiya, Murtaniya, Laberiya, Sudan ta Kudu, Gini, Saliyo, Malawi, Tarayyar Comoros da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
An kai allurai miliyan 70 zuwa Afirka inda aka yi amfani fa sama da miliyan 50.