Bayan jin karar harbe-harbe a kusa da Fadar Shugaban Kasar Nijar, an bayyana cewar an yi tunkurin juyin mulki wanda bai yi nasara ba.
Labaran jaridun Nijar sun bayyana cewa, gaf da asubahin ranar Larabar nan ne aka jiyo karar harbe-harbe a kusa da Fadar Shugaban Kasar da ke birnin Yamai, an bayyana hakan a matsayin yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba, an bayyana kama wasu jami'an sojin kasar.
Babu wata sanarwa da aka fitar a hukumance game da batun.
Majiyoyi sun bayyana cewa, rayuwa ta koma yadda ta ke a birnin Yamai.
Wannan lamari na zuwa a daidai lokacin da ake gaf da rantsar da sabon zababben Shugaban Kasar Nijar Mohamed Bazoum na jam'iyyar PNDS-Tarayya.
A ranar 2 ga Afrilu za a rantsar da Bazoum.