An yi wa dubunnan daruruwan yara allurar riga-kafin zazzabin cizon sauro a Afirka

A kasashen Afirka 3, an yi allurar riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro da aka samar a karon farko ga yara kanana sama da dubu 650.

Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa, a shekaru 2 da suka gabata an yi allurar riga-kafin zazzabin cizon sauro ga mutane miliyan 1,7 a Gana, Kenya da Malawi.

An bayyana yi wa yara kanana sama da dubu 650 allurar riga-kafin a kasashen 3.

Daraktar Riga-Kafi da Garkuwar Jiki ta WHO Katherine O'Brien ta shaida cewa, ana yin allurar ta RTS,S sau 4 ga wadanda ba su da garkuwar jikin da za ta hana kamuwa da zazzabin cizon sauro.

A karon farko a watan Afrilun 2019 aka fara yin allurar riga-kafin zazzabin cizon sauro a Malawi wadda cuta ce da ke kashe dubunnan daruruwan mutane a kowacce shekara.

A duk mintuna 2 cutar na kashe yaro krami 1, kuma an fi samun kamuwa da ita a kasashen Afirka.

 


News Source:   ()