A jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, an yi ruwan bama-bamai kan sansanin 'yan bindiga da suka yi garkuwa da dalibai. An bayyana kashe 'yan bindigar da dama.
Kwamishinan Harkokin Tsaron Cikin Gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya shaida cewa, sojoji sun kai farmaki a sansanin 'yan bindiga a yunkurin kubutar da daliban Kwalejin Kula da Gandun Daji ta Tarayya su 39 da aka yi garkuwa da su.
Aruwan ya ce, an lalata sansanin 'yan ta'addar a yayin farmakin, an kuma kashe 'yan bindiga da dama.
Aruwan ya kara da cewa, ana ci gaba da kai farmakai don kubutar da daliban su 39.
A ranar 12 ga Maris ne 'yan bindiga suka kai hari Kwalejin Kula da Gandun Daji ta Tarayya tare da garkuwa da mutane 210. An kubutar da 180 da suka hada da dalibai mata 42 da malamai 8.
A shekarar da ta gabata mutane 937 aka kashe a hare-haren 'yan bindiga tare da garkuwa da wasu 1972 a jihar Kaduna da ke arewa maso-yammacin Najeriya.
Tun daga watan Janairu zuwa yau 'yan bindiga suke ta kai hari kan makarantu tare da garkuwa da dalibai a arewacin Najeriya.