Kungiyar Hadin Kan Malaman Musulunci ta Duniya ta yi kira ga Faransa da ta daina tsoma hannu a al'amuran cikin gida na Chadi, sannan ta kwashe sojojinta ta bar kasar.
Shugaban Kungiyar Hadin Kan Malaman Musulunci ta Duniya Farfesa Ahmad Al-Raysuni da Sakatare Janar na Kungiyar Ali Muhyiddin Al-Karadag sun sanya hannu kan wata sanarwa wadda ta ce, akwai damuwa game da yanayin da aka shiga na rikici tsakanin 'yan adawa da gwamnatin soji ta rikon kwarya a Chadi.
Sanarwar ta yi kira ga Faransa da ta janye sojojinta daga Chadi ta kuma fice daga kasar tare da daina tsoma a hannunta a harkokin cikin gida na Chadi, sannan an bukaci gwamnatin sojin da ta shirya zabe ta hanyar zaman lafiya tare da daina kaiwa fararen hula masu zanga-zangar zaman lafiya hari.
Bayan mutuwar Shugaban Kasar Chadi Idris Deby Itno a filin daga yayin kai farmakai kan 'yan awaren FACT ne aka nada dansa Janaral Mahamat Idris Deby a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya ta soji.
Gwamnatin sojin ta bayyana wa'adin watanni 18 don gudanar da aiyukan mika mulki ga farar hula a kasar. A ranar 27 ga Afrilu aka nada tsohon Firaminista Pahimi Padacke Albert a matsayin Firaministan gwamnatin rikon kwaryar.
A yayin zanga-zangar adawa da gwamnatin sojin ta Chadi da aka yi a ranar 27 ga Afrilu an kashe mutane 6 tare da kama sama da 700.