An yi ikirarin sojoji sun kwace mulki a Mali

An yi ikirarin cewar a kasar Mali da ke fama da rikicin siyasa na wani dan lokaci, an jiyo karar harbe-harbe a wani barikin soji inda kuma aka tsare Ministoci da wasu manyan jami'an soji.

Labaran da jaridun kasar suka fitar bayan tattaunawa da shaidun gani da ido, na cewa an samu kai komo a barikin soji ta Kati da ke da nisan kilomita 15 daga Bamako.

An jiyo karar harbe-harbe, kuma daga cikin wadanda aka tsare har da SHugaban Majalisar Dokoki, Ministan Tattalin Arziki da Kasuwanci da na Kudi na Mali.

Ana kuma fadin cewar sojojin Mali sun kama wasu Ministocin daban.

'Yan adawar Mali sun bukaci Shugaban Boubakar Keita da gwamnatinsa su yi murabus inda suke jagorantar zanga-zanga a kasar.

Rahotanni sun ce shugaba Keita ya yi murabus, ya kuma rusa majalisar dokokin kasar bayan boren da sojoji suka yi.


News Source:   ()