A Mali, an yi garkuwa da mutane 4 da ke aiki tare da Kungiyar Likitocin Komai da Ruwanka (MSF).
Labaran da jaridun Mali suka fitar sun ce, wasu da ba a san ko suw aye ba ne suka yi garkuwa da ma'aikatan kungiyar ta MSF su 8 a wani karamin asibitin da ke yankin Mopti.
An saki mata 4 da ke cikin wadanda aka yi garkuwar da su, inda aka tafi da sauran mutane 4 maza 'yan kasar ta Mali.
Tun shekarar 2012 ake samun hare-haren ta'addanci a yankin Mopti na Mali.