An yi garkuwa da wasu ma'aikatan jirgin ruwa d8 da suka hada da 'yan kasar Labanan 3 a gabar tekun Najeriya.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Labanan ta fitar da rubutacciyar sanarwar cewa, jakadanta na Abuja Husam Diyab ya shaida mata an yi garkuwa da wasu ma'aikatan jirgin ruwan kasar da ke kan hanyar zuwa Kamaru daga Najeriya.
An bayyana cewar 'yan fashin tekun sun baiwa wasu 'yan Kamaru 2 damar komawa Najeriya da jirgin ruwan, amma sun tafi da mutane 8 da suka hada da 'yan kasar Labanan 2.
Jakadan Labanan a Abuja Diyab ya ce, tare da Rundunar Sojin Ruan Najeriya, suna bibiyar al'amuran sau da kafa.
Diyab ya ce, suna kuma tattaunawa da karamin jakadan Labanan da ke Kamaru.
An bayyana vewar jirgin ruwan ya tashi daga wani yanki da ke tsakanin Coss River da Kamaru bayan da wani kamfanin mai ya dauke hayar yin dakon mai daga kasar Kamaru.
Mısır'da yayınlanan El-Yevm es-Seba gazetesi ise kaçırılanlar arasında biri mühendis, diğeri subay 2 Mısırlı denizcinin de bulunduğunu yazdı.
Jaridar Al-Yaum A-Saba da ke Masar ta ce, daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su akwai Injiniya da Ma'aikata 2 'yan kasar Masar.