An yi garkuwa da dalibai da dama tare da malami guda a wata makarantar firamare da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya shaida cewa, wasu dauke da makamai a kan babura ne suka kai hari kan makarantar firamare ta kauyen Lea da ke yankin Birnin Gwari na jihar.
Aruwan ya tabbatar da an yi garkuwa da dalibai da dama da malami guda.
Kwamishina Aruwan ya kara da cewa, ba a gama tabbatar da dalibai nawa aka yi garkuwa da su ba, amma an aika da jami'an tsaro yankin.
A shekarar da ta gabata an kashe mutane 937 tare da garkuwa da dubu 1,972 a hare-haren da 'yan bindiga suka kai a jihar Kaduna.
Tun daga watan Janairu zuwa yau an yi garkuwa da dalibai a makarantu a kalla 5, wanda hakan ya sanya aka rufe makarantun kwana a wasu jihohin.
A ranar 12 ga Maris, 'yan bindiga sun kai hari kwalejin Tarayya ta Kula da Gandun Daji a Zamanance tare da yin garkuwa da mutane 219 da suka hada da mata 42 da malamai 8. An samu nasarar kubutar da 180 daga cikin su. Ana ci gaba da aiyukan kubutar da sauran dalibai 39.