Jam'iyyar MPS mai mulki ta shiga lunguna sa sako domin samun rinjaye, inda shugabanninta suka ce suna da burin lashe dukkan kujeru a majalisun dokokin kasar domin baiwa shugaba Mahamat karfin iko.
Jam'iyyar Les Transfomateur da ta zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa da ɗan takararta kuma tsohon Firaminista Success Masra sun kaurace wa zaɓen.
Zaben na zuwa ne watanni bakwai kacal bayan zaɓen shugaban ƙasa wanda ya tsawaita mulkin iyalan Deby a kasar mai arzikin mai a Tsakiyar Afirka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI