Dubunnan mutane sun halarci bukin murnar nasarar cimma matsaya a watan da ya gabata tsakanin gwamnatin rikon kwarya ta Sudan da 'yan a ware da ke dauke da makamai tsawon shekaru a kasar.
Dubunnan Sudanawa da ke yankuna daban-daban sun halarci dandalin 'Yanci da ke Khartoum Babban Birnin Kasar dauke da tutocin kungiyoyin da suke ma biyayya.
'Yan kasar ta Sudan sun yi rawa da wakoki na gargajiya, sun yi kira ga hadin kai tare da yin kalaman nuna adawa ga yaki.
A ranar 3 ga watan Oktoba a Juba Babban Birnin Sudan ta Kudu, gwamnatin rikon kwarya ta Sudan ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da wasu kungiyoyin 'yan a ware masu dauke da makamai da yawa da suka hade karkashin 'Inuwar Juyin Juya Hali'.