A makon da ya gabata majalisar wakilan ƙasar ta kaɗa kuri’ar tsige Gachagua, wanda ya taimaka wa shugaba William Ruto wajen ɗarewa ƙujerar shugabanci shekaru 2 da su ka wuce, amma kuma ya ke shan caccaka daga muƙarraban shugaban, bisa zargin rashin mmubayi’a da furta kalamai masu kawo rarrabuwar kawuna.
54 daga cikin ƴan majalisar dattawar 67 ne su kaɗa ƙuri’ar tsige Gachagua a kan laifin saba wa kundin tsarin mulki, fiye da 2 bisa 3 da doka ta tanada kenan, lamarin da ya maishe shi shugaba ko mataimaki na farko da aka taɓa kora tun bayan da aka sanya batun tsigewa a kudin tsarin mulkin ƙasara a shakarar 2010.
Majalisar dattawar ta kaɗa wannan kuri’ar ce duk da cewa tun da farko a ranar Alhamis, an garzaya da matamakin shugaban asibiti sakamakon tsananin ciwon ƙirji da ya kama shi, sun yi haka ne ba tare da sauraron uzurin lauyansa ba, duk kuwa da ya gabatar da shi.
Laifuka 11 da ake zargin Gachagua da aikatawa, waɗanda ya musanta, sun haɗa da rashawa, halasta kuɗaden haram, yin siyasar ƙabilanci da sauransu.
Masu sharhi dai sun danganta abin da ya sami Gachagua da bita-da-ƙullin siyasa, su na mai cewa ƙaiƙayi na iya komawa kan masheƙiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI