An tsare gommai masu zanga zanga yaki da cin hanci da rashawa a Ghana

An tsare gommai masu zanga zanga yaki da cin hanci da rashawa a Ghana

An soma kamen ne da sanyin safiyar jiya  lahadi lokacin da masu zanga zanga suka so kawo cikas a kokarin ‘yan sanda na tabbatar da doka da oda kamar yadda daraktan yada labaran runduna ‘yan sanda Ghana Grace Ansah Akrofi ta sanar , tana mai  bayyana taron amatsayin wanda ya sabawa doka.

Bayan lafawa rana,  wasu gommai masu zanga zanga sun yanke shawara  sake dawowa akan tituna.

Guda daga cikin masu zanga zanga Felicity Nelson cikin hushi ta fada cewa, baya daga  hurumin ‘yan sanda na zaba mana inda ya kamata mu gudanar da zanga zanga hakki ne da kundin tsarin mulkin kasar ya bamu.

Wadanda suka shirya zanga zangar sun zargi gwamnati da tauye wa jama’a ‘yancin fadin albarkacin baki, yayin da suka ce an kame jumullar mutane 32 ciki har da wata karamar yarinya ‘yar shekaru 8 da haihuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)