A gabar tekun kasar Tunusiya an tsamo gawarwakin bakin haure 21.
Kakakin Dakarun Tsaron Kasa na Tunisiya Husameddin Jibali ya shaida cewa, an sake samun gawarwakin bakin haure 21 a gabar tekun garin Sfaks bayan hatsarin jiragen ruwa 4 da ya afku a kwanaki 10 da suka gabata. Ya zuwa adadin wadanda aga gano jikkunansu ya kai mutane 49.
Jibali ya kara da cewa, an kubutar da mutane 78 sakamakon hadurran, kuma kwai mutane 135 a cikin jiragen inda wasu 8 suka bata.