An tsamo gawarwakin ƴan cirani 27 da jirgin ruwansu ya a Tunisia

An tsamo gawarwakin ƴan cirani 27 da jirgin ruwansu ya a Tunisia

A cewar babban jami’in da ke kula da gabar tekun Zied Sdiri, sun gano gawarwakin ƴan ciranin da lamarin ya rutsa da su ne a tsibirin Kerkennah, kuma sun fito ne daga yankin yammacin Sahara.

Sdiri ya ce 15 daga cikin wadanda suka ceto an garzaya da su asibiti duk da dai bayyi ƙarin bayani kan hakan ba.

Wani jami’in rundunar da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, ƴan ciranin su 110 sun yi ƙoƙarin yin amfani da ƙananan jiragen ruwan don silalewa cikin daren Talata su tsallaka Turai.

Ƴan cirani daga Afrika dai na amfani da Tunisia da kuma makwabciyarta Libya don tsallakawa Turai, duk kuwa da hatsarin da hakan ke da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)