Ƴan tawayen Nijar da Mali sun ƙulla ƙawancen gwagwarmaya da taimakon juna

Ƴan tawayen Nijar da Mali sun ƙulla ƙawancen gwagwarmaya da taimakon juna

Kakakin CSP Mohamed Elmaouloud Ramadan ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa tun a ƙarshen watan Agusta ne ɓangarorin biyu suka ƙulla ƙawancen yayin wani taro da suka gudanar a garin Tinzaouatene da ke gab da iyakar Algeria.

Dukkanin ɓangarorin ƴan tawayen biyu na Mali da Nijar yanzu haka na gwabza yaƙi ne da gwamnatocin Bamako da Yamai, ƙasashen da ke ƙarƙashin mulkin Sojoji tun bayan tsanantar ayyukan ƴan ta’adda.

A cewar Elmaouloud Ramadan wakilcin ƙungiyarsu ta CSP ya gana da tawagar ƴan tawayen na Nijar ƙarƙashin jagorancin babban kwamandan ƙungiyar ta EPL a Tinzaoutene inda suka gudanar da taron haɗaka tare da ƙulla ƙawance tsakanin ranakun 25 zuwa 29 ga watan Agusta.

Ƙungiyar ta CSP mai ɗauke da galibin ƴan tawayen Tuareg da ke ƙaddamar da hare-harensu a iyakar Algeria ko a baya-bayan nan su suka jagorancin harin da ya hallaka tarin Sojojin Mali da na Wagner tare da kame wasu a matsayin fursunonin yaƙi.

A ɓangare guda ƙungiyar EPL a Nijar wadda yanzu haka ke yiwa gwamnatin Sojin ƙasar tawaye tare da neman sakin hamɓararren shugaban ƙasar Bazoum Mohamed ta tabbatar da wannan ƙawance tsakaninta da CSP a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)