Ƴan tawayen Mali sun ce har yanzu suna tsare da tarin Sojin hayar Wagner

Ƴan tawayen Mali sun ce har yanzu suna tsare da tarin Sojin hayar Wagner

Kakakin ƙungiyar ƴan tawayen ta CSP mai rajin tabbatar da tsaro da zaman lafiyar ƙasar ta Mali Mohamed Elmaulud Ramadane ya shaidawa Reuters cewa fursunonin na cikin ƙoshin lafiya kuma ƙofa a buɗe ta ke don fara tattaunawa kan makomarsu.

A watan jiya ne ƴan tawayen na Tuareg suka sanar da kisan Sojin hayar Wagner 84 da wasu Sojin Mali 47 a wani gumurzu da suka shafe kwanaki suna yi akan iyakar ƙasar tsakaninsu.

Haka zalika sun sanar da kame wasu da dama da yanzu haka ke tsare a matsayin fursunan yaƙi.

Wasu bayanai sun ce bayan da mayaƙan ƴan tawayen suka yi nasara kan dakarun Malin da na Sojin hayar Wagner ne kuma, suka riƙa ɗaga tutar Ukraine, dalilin da ya sanya gwamnatin Sojin ƙasar zargin hannun Ukraine wajen taimakawa ayyukan ta'addanci a ƙasar ta yankin Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)