Ƴan tawayen M23 sun fara fuskantar turjiya daga dakarun Congo a Goma

Ƴan tawayen M23 sun fara fuskantar turjiya daga dakarun Congo a Goma

Kwana guda bayan da ƴan tawaye su ka kutsa cikin birnin da ke gefen tafkin Kivu, masu zanga-zanga sun kai farmaki cikin harabar  ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya  da ofisoshin jakadanci da su ka haɗa da na Rwanda, Faransa  da Amurka, su na mai bayyana ɓacin rai a kan abin da su ka kira  katsalandan daga waje.

A ranar Litinin da ta gabata mayaƙan M23 su ka shi ga birnin Goma, a fito-na-fito mafi muni tun daga shekarar 2012 na cikin rikicin da aka shafe shekaru 30 ana yi, wanda ya samo asali daga kisan ƙare dangi na Rwanda da kuma rikicin wanda zai yi  iko da ɗimbin albarkatun ƙasa da  Congo ke da su.

Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta ce dakarun Rwanda su na cikin birni Goma, inda su ke taimaka wa ƴan tawayen M23, a yayin da Rwand ata kare kanta tana cewa makatakan kariya ta ke ɗauka saboda barazanar da ta ke fuskanta daga ƴan tsagera a Congo.

Gwamman daakarun Jamuriyar Dimokaradiyyar Congo sun miƙa wuya, amma wasu sojoji da mayaƙan sa kai su na ci gaba da turjiya, a cewar mazauna yankin da wasu majiyoyin Majalisar Ɗinkin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)