Ƴan tawayen M23 da ke kawance da sojojin Rwanda sun kama birnin Bukavu

Ƴan tawayen M23 da ke kawance da sojojin Rwanda sun kama birnin Bukavu

Da samun labarin kwace wannan birni, shugaban na Congo ya soke batun halartar taron kungiyar Tarayyar Afirka a a kasar Habasha.

Bayan kwace Goma, babban birnin lardin Kivu ta Arewa, a wani farmakin walkiya a karshen watan Janairu, mayaka daga kungiyar M23 masu dauke da makamai da kuma ke samun rakiyar sojojin Rwanda sun ci gaba da shiga lardin Kivu mai makwabtaka da kasar.

Goma, República Democrática do Congo, 6 de Fevereiro de 2024. Yan Tawayen M23 a birnin Goma AFP - MICHEL LUNANGA

 A cewar majiyoyin tsaro da na jin kai, kungiyar ta M23 sun shiga yankunan da ke arewa maso yammacin Bukavu, babban birnin Kivu ta Kudu, kusan ba tare da fuskantar wata adawa daga sojojin DRCongo.

Yan Tawayen M23 a Bukavu Yan Tawayen M23 a Bukavu © Amani Alimasi / AFP

'Yan sa'o'i kadan da suka gabata, 'yan kungiyar dauke da makamai sun karbe iko da filin tashi da saukar jiragen sama na lardin, wani muhimmin wuri inda aka ajiye sojojin Congo (FARDC) da ke da tazarar kilomita talatin daga birnin. Shagunan birnin sun kasance a rufe. Wakilan kungiyoyin fararen hula, a cikin wata wasika da suka aike wa hukumomin yankin a cikin 'yan kwanakin nan, sun yi kira ga sojojin da kada su "fada cikin rikici a cikin birni" don guje wa "kisan mutane". A cewar wata majiyar tsaro, dakarun FARDC da na Burundi da aka tura yankin domin tallafawa Kinshasa, galibi sun janye zuwa kudu maso gabashin Bukavu zuwa kan iyaka da Burundi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)