Da ya ke karba tsaffin ƴan tawayen da suka ajiye makamai, gwamna Jihar Agadas Janar Ibrah Boulama ya ce an cimma wannan nasarar ce sakamakon shiga tattaunawa da wasu fitattun mutane sukayi da ƴan tawayen ƙungiyar ta FPL a farkon watan Nuwamban nan da muke ciki.
Tun farko ƙungiyar ta FPL ta kasance mai adawa da gwamnatocin biyu da suka shude ƙarskashin ikon PNDS Tarayya kafin daga bisani ta rikide zuwa mai goyawa Bazoum Mohamed da sojoji suka kifar a watan Yulin 2023, tare da nema a sake shi cikin gaggawa.
A rana 1 ga watan Nuwamba kakakin ƙungiyar Idrisa Madaki da wasu mutane uku suka mika kansu ga gwamnatin mulkin sojin Nijar kamar yadda majiya soji ta tabbatar.
Cikin wata hira da ya yi da gidan talabijin mallakin gwamnati RTN a rana 11 ga wanan watan, Madaki ya nemi afuwa shugaban gwamanatin mulkin sojin Nijar Janar Abdurahmane Tiani da kuma al’umma bisa kuskuren da ya aikata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI