An tabbatar da nasarar Tebboune da kashi 84% na kuri'un da aka kada a Algeria

An tabbatar da nasarar Tebboune da kashi 84% na kuri'un da aka kada a Algeria

Ta bakin Shugaban shugaban kotun tsarin mulkin, Omar Belhadj "muna sanar da cewa Abdelmadjid Tebboune an zabe shi a matsayin shugaban kasa a karo na biyu kuma zai fara aiki da zarar an rantsar da shi."

Shugaban kotun na fadar haka ne kai tsaye ta gidan talabijin da gidan rediyon kasar.

Bisa kididdigar da aka yi na farko, hukumar zaben Anie ta sanar a ranar Lahadin da ta

Takardar zaben Algeria Takardar zaben Algeria © AFP

gabata cewa Shugaba Tebboune ya samu nasara, da kashi 94.65% na kuri'un da aka kada. Shugaban kasa mai barin gado, wanda ya fafata da ‘yan takara biyu da ba a san su ba, ya samu tagomashi sosai saboda ya kuma amfana da goyon bayan wasu muhimman kungiyoyin siyasa guda hudu da suka hada da National Liberation Front (FLN).

Takardun zaben kasar Algeria Takardun zaben kasar Algeria AFP - -

A watan Disamba na 2019, an zabe shi da kashi 58% na kuri'un, a wani lokaci da aka fuskanci tashin hankali a kasar ta Algeria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)