Tun a Lahadin da ta gabata ne wasu sassa na Mozambique suka fara fuskantar mummunar guguwar, ko da ya ke sai a jiya Litinin ne ta fara yin gagarumar illa tare da kashe mutanen 34.
Hukumar OCHA ta ce yanzu haka akwai dubban ɗaruruwan mutane da ibtila’in ya ɗaiɗaita a gabashin ƙasar ta kudancin Afrika.
Ibtila’in guguwar na zuwa bayan faruwar makamanciyarta a tsibirin Mayotte wadda bayanai ke cewa ta hallaka ɗaruruwa ko kuma dubbban mutane duk da cewa babu sahihan alƙaluman daga mahukuntan yankin.
Sanarwar da hukumar OCHA ta fitar ta ce baya ga mutane 34 da suka mutu, ƙaƙƙarfar guguwar ta kuma shafi adadin mutane dubu 174 da 158 a Mozambique yayin da ta jikkata wasu 319.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Mozambique ke fuskantar ibtila'in guguwa cikin shekarar nan ba, domin ko a baya-bayan nan guguwar ta hallaka tarin mutane wanda ya tilasta kwashe al'ummomin da ke zaune a gab da tsaunuka ko kuma bakin ruwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI