Ƴan ta'adda sun kashe dakarun Togo 10 a iyakar ƙasar da Burkina Faso

Ƴan ta'adda sun kashe dakarun Togo 10 a iyakar ƙasar da Burkina Faso

Rahotanni sun ce sojojin da aka kai wa hari na tsaka da kula da wani aikin ganuwa na tsaro da ake yi dan hana kungiyoyin yan ta’adda samun damar kai wa alumma hari.

Da farko bayanai sun nuna akalla mutane 19 aka kashe, wato, sojoji 9 da fararen hula 10, wadanda aka dauka aiki dan gina ramukan, saboda ya zama shinge tsakaninsu da ‘yan ta’adda..

Tuni dai aka alakanta harin da kungiyar Alqaeda, duk kuwa da cewa babu wanda ya dauki alhakin sa, ganin cewa kungiyar ta dauki alhakin kai mumunar harin ranar 20 ga watan yulin da ya gabata a wani sansanin soji da ke kusa da kan iyakar Burkina Faso.

Hukumomin Togo dai sun kara tsaurara tsaro a kan iyakar kasar da Burkina Faso domin kauce wa yiwuwar sake faruwar hakan nan gaba, kuma daga cikin matakan tsaro da aka dauka akwai taƙaita zirga zirga, gudanar da kwakwarar bincike a kan motoci masu wucewa da kuma sanya dokar ta baci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)