Majiyoyin da suka hada da na jami'an tsaron Ghana da jami'an diflomasiyyar yankin, sun ce da alama mahukuntan Ghana sun kauda kai, kan yadda ƴan tada kayar bayan da ke tsallakowa daga makwabciyarta Burkina Faso domin tara kayan abinci da man fetur da ma ababen fashewa, tare kuma da samarwa mayakansu da suka jikkata wuraren kula da lafiyarsu a asibitoci.
Jakadan Ghana a Burkina Faso Boniface Gambila Adagbila, ya shaidawa Kamfanin Dillacin Labarai na Reuters cewa mayakan na amfani da iyakokin ƙasar don samun mafaka, sai dai ya musanta zargin da ake yi cewa mahukuntan ƙasar sun cimma yarjejeniyar hana kai hari kan ƴan ta’adda, inda ya ce ƙasashen na Ghana da Burkina Faso na aiki tare don fatattakarsu.
Burkina Faso ta rasa iko da fiye da rabin yankunanta yayin da ƙungiyar JNIM da ke samun goyon bayan al Qaeda ke samu galaba.
A wata tattaunawa da fitattacen ɗan Jaridar RFI sashen Faransanci Wassim Nasr yayi da Hamadoun Kouffa shugaban ƙungiyar JNIM, ya shaida masa cewa suna da niyar faɗaɗa hare-harensu zuwa ƙasashen Ghana da Togo da kuma Jamhuriyar Benin.
Ghana na da iyaka mai nisan kilomita dari 6 da Burkina Faso, wacce ke fama da matsalolin ƴan ta’adda da suka kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI