Jami’in yaɗa labarai na fadar shugaban ƙasar Angola, Mario Jorge ya bayyanawa manema labarai cewa, bazaiyu a yi zaman da aka shirya yi a ƙasar tsakanin shugabannin Rwanda da Congo.
Jorge ya ce shugaban Angola wanda kuma shi ne jami’in da ke shiga tsakani a madadin ƙungiyar tarayyar Afrika, Joao Lourenco na tattaunawa da shugaban Congo, Felix Tshesekedi.
An yi tsammanin cewa shugaba Paul Kagame na Rwanda zai halarci zaman, sai dai babu tabbacin ko ya isa Angola.
Ana sa ran tattaunawar za ta kawo ƙarshen rikicin gabashin Congo, inda ƙungiyar ƴan tawayen M23 da Rwanda ke goyawa baya ta kwace yankuna da dama, wanda hakan ya raba dubban mutane da muhallansu, abinda ya ƙara ta’azzara buƙatar ayyukan jin ƙai.
Faɗar shugaban ƙasar Congo ta ce an wargaje tattaunawar ne bisa buƙatar da Rwanda ta kawo na cewa sai dai Congon ta tattauna kai tsaye da ƴan tawayen M23.
Tun bayan dawowar ayyukanta a shekarar 2021, ƙungiyar ƴan tawayen M23 wadda akasarin mambobinta ƴan ƙabilar Tutsis ne da ke iƙirarin kare muradansu, ta kwace yankuna da dama a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, wanda hakan ya ta’azzara rikice-rikice a yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI