An shawo kan gobarar dajin da ta kama a Aljeriya

An shawo kan gobarar dajin da ta kama a Aljeriya

Aljeriya ta bayyana shawo kan dukkan gobarar dajin da ta kama a 'yan kwanakin da suka gabata a kasar.

Cibiyar Tsaron Fararen Hula ta Aljeriya ta sanar a cewa, a awanni 24 da suka gabata an sake kashe gobara 7 a dazuka 6 na kasar, kuma ba a sake samun labarin ganin gobarar daji a kasar ba.

Aljeriya ta sha fama da gobarar daji a kwanaki 10 da suka gabata a yankuna masu tsaunuka da ke arewaci da arewa maso-gabashin kasar.

A kalla mutane 70 da suka hada da sojoji da fararen hula ne suka mutu a Aljeriya sakamakon gobarar dajin da ta kama a garuruwa 18.


News Source:   ()