Rahotanni daga Sudan sun ce gwamnatin rikon kwarya ta kasa ta sauke Ministan Lafiya Ekrem Ali Al-Tum daga mukaminsa.
Sanarwar da aka fitar daga Majalisar Mulki ta Sudan ta rawaito Shugabanta Janaral Abdulfatah Al-Burhan na cewa, Firaminista Abdullah Hamduk, wasu mambobin majalisar da jami'an gwamnati sun jefa kuri'ar amincewa da sauke Al-Tum daga mukaminsa.
Sanarwar ba ta bayar da dalilin sauke Ministan ba.
Amma sanarwar da bangaren gwamnati ya fitar ta ce ba a cimma matsaya ba game da sauke Ministan, kuma ba a bayar da shawarar a sauke shi ba.
Kakakin gwamnatin Sudan Faisal Muhammad Salih ya ce babu wata matsaya da aka cimma da gwamnatinsu game da sauke Ministan na Lafiya na Sudan. Kawai a yayin taron Majalisar Mika Mulki ne wasu suka bayar da shawarar a cire Ministan Lafiyar.