An sanya Gandun Dajin Ivindo na Gabon a jerin abubuwan tarihi na UNESCO

An sanya Gandun Dajin Ivindo na Gabon a jerin abubuwan tarihi na UNESCO

An saka Gandun Dajin Ivindo wanda ke Gabon, daya daga cikin kasashen Afirka cikin jerin abubuwan tarihi na UNESCO (Hukumar Kyautata Ilimi, Kimiya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya).

A cikin rubutacciyar sanarwa daga UNESCO, Ivindo daya daga cikin manyan wuraren shakatawa na kasar, yana dauke da dabbobi da tsirrai iri-iri. An ba da rahoton cewa, wurin shakatawan wanda ke da fadin hekta dubu 300, an saka shi cikin jerin abubuwan tarihi na duniya.

A cikin gandun dajin Ivindo, inda akwai koguna da rafuka, akwai nau'ikan dabbobi da yawa kamar giwaye, gwaggwan biri da damisa gami da nau'ikan shuke-shuke daban-daban.

Gabon wacce ke da wuraren shakatawa 13 na kasa wanda ya kai kashi 11 cikin dari na yankin, yana da wuraren da aka adana 20.

Har ila yau kasar na da kaso 60 cikin 100 na giwayen daji na Afrika da ke cikin hadari.

A karon farko a Gabon, an saka Lope National Park a cikin jerin abubuwan tarihi na UNESCO a shekarar 2007.


News Source:   ()