An sanya dokar hana fita a wasu jihohi 3 na Najeriya

Sakamakon yawaitar hare-haren 'yan bindiga, an saka dokar hana fita a jihohin Rivers, Ebonyi da Anambra da ke kudancin Najeriya.

Gwamnan jihar Rivers Ezenwo Nyesom Wike ya sanar da cewa, sakamakon rikicin da ake samu a jihar an aiyana dokar hana fita waje a yankuna 28 har lokacin da aka sake fitar da wata sanarwar.

Gwamnan jihar Anambra Willie Obiano ma ya sanar da cewa, an saka dokar hana fita waje sakamakon rikicin da akesamu tsakanin 'yan ta'addar Biafra da al'umar Hausa-Fulani.

Obiano ya kara da cewa, an aika da jami'an tsaro zuwa yankunan jihar daban-daban.

Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi kuma ya sanar da cewa, an saka dokar hana fita ta kwanaki 3 a jihar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gudanar da taron majalisar zartarwa a Abuja sakamakon yawaitar hare-hare a kasar.

A mako dayan da ya gabata 'yan bindiga sun kashe mutane 239 tare da garkuwa da wasu 44 a Najeriya.


News Source:   ()