Ƴan sandan Mozambique sun kashe masu zanga-zangar 11 tare da jikkata 50

Ƴan sandan Mozambique sun kashe masu zanga-zangar 11 tare da jikkata 50

Dubban masu zanga-zanga ne suka fantsama a biranen ƙasar ta kudancin Afrika don ƙalubalantar nasarar Daniel Chapo, ɗan takarar jam’iyyar ta Frelimo wadda ke mulkin ƙasar tun bayan samun ƴanci a shekarar 1975.

Galibin masu zanga-zangar waɗanda ko dai mambobin jam’iyyun adawa ne ko kuma magoya baya, sun yi arangama da jami’an ƴan sandan waɗanda aka ɗorawa alhakin kawar da jama’a daga kan tituna, aragmar da HRW ke cewa ta kai ga asarar rayukan jama’a.

Ƴan sanda yayin arangama da masu zanga-zanga. Ƴan sanda yayin arangama da masu zanga-zanga. © Siphiwe Sibeko / Reuters

HRW ta ce daga ranar 24 zuwa 25 ga watan nan ne aka yi arangamar inda ƴan sanda suka hallaka mutane 11 tare da jikkata sama da 50 ko da ya ke suma jami’an ƴan sandan 8 sun samu raunuka.

Ƙungiyar ta HRW ta ce a tattaunawar da ta yi da mutane 22 da suka ƙunshi shaidun gani da ido, da jami’an lafiya da kuma ƴan jarida baya ga ƴan ƙungiyoyin fararen hula da kuma wasu jami’an gwamnati ta samu tabbacin irin cin zarafin da fararen hula suka fuskanta yayin gangamin.

A cewar Human Right Watch hatta ƙananun yara ƴan ƙasa da shekara guda, cin zarafin ƴan sandan bai barsu ba, inda da dama suka galabaita bayan shaƙar barkono tsohuwar da jami’an tsaron suka riƙa harbawa a lungu da saƙon anguwannin jama’a.

Ƙungiyar ta ce da dama cikin waɗanda suka samu raunuka an harbe su ne kai tsaye da nufin hallakasu ciki har da wanda harsashi ya taɓa lakarshi wanda ke nuna ke nuna abu ne mai matuƙar wahala ya murmure ya dawo kamar a baya.

Rahotanni sun ce ƴan sandan sun kame mutanen da ya yawansu ya haura 450 waɗanda yanzu haka su ke tsare a hannun mahukuntan ƙasar kawai don sun fita zanga-zangar ƙalubalantar sakamakon zaɓe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)