Mutanen biyu da aka bayyana sunansu da Jasten Mabulesse Candunde mai shekaru 42 da kuma wani shugaban ƙauye Leonard Phiri mai shekaru 43 an kame su ne a birnin Lusaka fadar gwamnatin ƙasar ɗauke da hawainiya mai rai wadda da ita ce suke shirin yiwa shugaban ƙasar asiri.
Sanarwar da rundunar ƴansandan ta Zambia ta fitar ta ce tun a Juma’ar da ta gabata aka kema mutanen 2 waɗanda bincike ya gano cewa dama suna aikata siddabaru kasancewarsu bokaye a yankunan da suka fito.
A cewar rundunar ƴan sandan tun farko wani ɗan uwan ɗan majalisar ƙasar na jam’iyyar adwa ne ya yi hayar mutanen biyu don aiwatar da aika-aikar wajen yiwa shugaba Hichilema asiri.
Bayanai sun ce ɗan Majalisar jam’iyyar adawar na fuskantar tuhuma ne kan hannu a fashi da makami da kuma yunƙurin kisan kai.
A cewar rundunar ƴan sandan kowanne lokaci daga yanzu mutanen biyu za su bayyana gaban kotu don amsa laifuka masu alaƙa da yunƙurin cutar da shugaban ƙasar ta hanyar sihiri baya ga azabtar da dabbobi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI