An sanar da zaman makoki na kwanaki 3 a Mali sakamakon harin ta'addancin da aka kai a arewacin kasar tare da kashe sojoji 33.
Sakamakon kisan sojojin da aka yi a garin Tessit an sanar da zaman makoki na kwanaki 3 da suka fara daga ranar Alhamis din nan.
A ranar Litinin ne aka kai hari a yankin Ansango na arewacin Mali inda aka kashe sojoji 33, an bayyana kashe 'yan ta'adda 20 da suka kai harin.
Ana bayyana harin a matsayin wanda dakarun Mali suka rasa jami'ai mafi yawa.
A farkon watan Fabrairu ma an kai hari a yankin Mopti na Mali tare da kashe sojoji 10.