An sanar da zaman makoki na kwanaki 2 a Jamhuriyar Nijar

An sanar da zaman makoki na kwanaki 2 a Jamhuriyar Nijar

An sanar da zaman makoki na kwanaki 2 a Jamhuriyar Nijar sakamakon harin ta'addanci da aka kaia iyakar kasar da Mali tare da kashe mutane 37.

Kakakin gwamnatin Nijar Badoulkadri Tidjani ya shaida cewa, zaman makokin na awanni 48 ya fara daga daren Talatar nan.

A ranar 16 ga Agusta ne wasu da ba a san ko su waye ba suka kai hari a kauyen Derey Dey na yakin Tillaberi inda suka kashe mutane 37 da suka hada da mata 4 da yara kanana 14.

A ranar 26 ga Yuli ma an kai hari kauyen Derey Dey tare da kashe fararen hula 16.


News Source:   ()