An bayyana cewa a rikicin da aka fara a ranar 3 ga watan Afirilu a garin Jineyne dake Yammacin Darfur a kasar Sudan kawo yanzu mutum 50 sun rasa rayukansu inda wasu 132 suka raunana.
An rufe hanyoyin Kudancin Jineyne tare da kuma dakatar da kai dukkanin gudunmowa a yankin.
Kwamitin Likitocin Yankin Yammacin Darfur sun sanar da cerwa an kaiwa motar dake dauke da wadanda suka raunana hari lamarin da ya yi sanadiyar raunanan ma'aikatan lafiya uku.
Haka kuma Walin Yammacin Darfur ya yi kira ga al'umman yankin da su kasance a cikin gidajensu har sai an samar da lumana a yankin.
Kasar da ta kasance al'umma nada makami a hannunsu na tsawon lokaci sun kasance suna yana fadace-fadace akan rikicin gonaki, filaye da ruwan sha.