An samu karuwa masu fama da matsala tamowa a Najeriya:ICRC

An samu karuwa masu fama da matsala tamowa a Najeriya:ICRC

Rahotan da kungiyar ICRC ta fitar ya ce cibiyoyin kula da lafiyar sun sanar da samun karuwar akalla kashi 24 na yawan yaran dake fama da karancin abinci mai gina jiki sabanin adadin da aka gani a shekarar da ta gabata.

Hukumar na danganta wannan matsalar da matsalolin da suka addabi yankin irin na tashe tashen hankula da kuma farin da ya hana mutane samun abinci mai gina jiki da za su ciyar da yaran su.

Wata mata da ake kira Rabiatu Jibrilla ta ce lokacin da ta kai yaron ta cibiyar kula da lafiyar ko zama baya iya yi, yayin da cikin sa ya shanye kamar babu hanji a ciki.

ICRC ta ce a watanni 3 na biyun wannan shekara ta yi rajistar karin yaran da suak kai kashi 48 da ke fama da tsananin rashin abinci mai gina jiki wadanda ke kasa da shekaru 5 a asibitocin da suke taimakawa sabanin abinda aka gani bara.

Kungiyar ta ce akalla yara miliyan 6 da dubu 100 a yankin Tafkin Chadi ke fuskantar barazanar karancin abinci mai gina jiki a watanni maus zuwa saboda ci gaba da tashin hankalin da ake fuskanta da kuma matsalar sauyin yanayi, adadi mafi girma da aka taba gani a cikin shekaru 4 da suka gabata.

ICRC ta ce tashin hankalin da ake fuskanta a yankin wanda ya sake ta'azzara a watanni 6 na farkon wannan shekarar shine dalilin fuskantar wannan yanayi mafi muni na karancin abinci, ganin yadda ya raba miliyoyin mutane da gidajen su da lalata hanyoyin sana'oin su tare da shafar noman da ake yi domin samun abinci.

Wani manomi da ake kira John Paul Ezra yace yanzu ba su da isassun filayen noma kamar yadda suke yi a shekarun baya saboda wannan matasalar ta tashe tashen hankula wadanda suka hana mutane zuwa gonakin dake nesa da gari a Madagali dake jihar Adamawa.

Shi kuwa Abubakar Bello Duhu dake kauyen Kwata Kwamla ya ce dogara da mutanen yankin suka yi da noman damina ya gamu da matsalar karancin ruwan sama wanda ya shafi abinda suke nomawa, ya yin da ambaliya kuma ke illa a wasu yankunan.

Kungiyar agaji ta ICRC na aiki tare da Red Cross a tsakanin al'ummar da ke yankin tare da  kananan hukumomi domin tallafa musu da kudaden da za su samar da irin dake jure fari da kuma maganin rigakafi na dabbobin su.

Shugaban tawagar ICRC a Mubi, Francesca Piccin ta ce suna kokarin inganat taimakon da suke bai wa jama'ar yankin, sai dai bukatun jama'ar ya zarce abinda suke ba su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)