An sami wasu muhimman bayanai cikin jirgin da ake zargin dakarun RSF sun kakkaɓo a Sudan

An sami wasu muhimman bayanai cikin jirgin da ake zargin dakarun RSF sun kakkaɓo a Sudan

Dakarun dake karawa da sojojin Sudan a yaƙin, sun bayyana cewa an samu wasu takardu da ke ƙunshe da muhimman bayanai a cikin jirgin.

Haɗarin dai ya ba da tabbaci akan irin hanyoyin da ake bi wajen samar da bayanai masu cike da ruɗani a yaƙin da aka shafe sama da watanni 18 ana fafata yaƙi a tsakanin sojojin Sudan da dakarun ɗaukin gaggawa na RSF.

Yaƙin ya jefa mutane sama da miliyan 11 cikin fitina tare da haifar da matsananciyar yunwa kuma ya ja hankalin ƙasashen duniya.

Wani bincike da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi kan takardun da aka samu a cikin jirgin da faifan bidiyo da kafofin sada zumunta suka yaɗa, ya nuna cewa an taɓa samun ɗaya daga cikin ma'aikatan jirgin ɗan ƙasar Rasha da aikata laifin safarar makamai.

A ɗaya ɓangare kuma dakarun RSF sun yaɗa wani faifan bidiyo da ke nuna dakarunta a tsaye a kusa da ɓaraguzan jirgin, da suka ce sun harbo a Al-Malha na arewacin Al-Fashir da sanyin safiyar ranar Litinin.

Kana rundunar ta RSF ta kuma yaɗa wasu hotuna da ke nuna alamun wasu ƴan ƙasar Rasha biyu da ta ce suna cikin jirgin tare da wasu sojojin Sudan uku, a yayin da rundunar tace ana amfani da jirgin ne wajen ɗaukar makamai da ake kaiwa sojoji a Al-Fashir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)