An samar da alluran riga-kafin Corona a Najeriya

An samar da alluran riga-kafin Corona a Najeriya

A Najeriya, an sanar da kirkirar alluran riga-kafin cutar Corona (Covid-19) har guda biyu.

Sakataren Gwamnatin Tarayya Kuma Shugaban Kwamitin Yaki da Annobar Boss Mustafa ya sanar da cewa, malaman kimiyya a kasar sun samar da alluran riga-kafin Corona a karon farko.

Mustafa ya ce, ana ci gaba da gwaje-gwajen alluran a dakin bincike.

Ya ce, "Da zarar an gama gwajin alluran an kuma samu takardar amincewa za a fara amfani da su. Wannan cigaba ne da zai kara habaka kimar Najeriya a fagen kimiyya da bincike."

Mustafa ya yi kira ga hukumomin Najeriya da su bayar da dukkan goyon bayan da kamfanunnukan da suka samar da alluran su ke bukata.

Najeriya ta karbi alluran riga-kafi guda miliyan 4 da dubu 224 a karkashin Shirin Covax na kasa da kasa da ya ke rabawa kasashe marasa galihu alluran.


News Source:   ()