A jihar Kaduna ta Najeriya, an sako wasu dalibai 14 da wasu ‘yan bindiga suka sace daga wata jami’a mai zaman kanta a ranar 20 ga watan Afrilu.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida Samuel Aruwan ya sanar da sakin dalibai 14 da aka sace daga Jami’ar mai zaman kanta ta Gandun Daji (Green Field) .
Aruwan ya bayyana cewa daliban da bai bayar da bayani game da yadda aka sake su ba an mika su ga iyalansu.
‘Yan bindiga sun sace dalibai 19 a wani hari da suka kaiwa jami’ar mai zaman kanta ta Green Field a ranar 20 ga watan Afrilu. Biyar daga cikin wadannan daliban an tsinci gawar su ne kusa da makarantar a ranar 23 ga Afrilu.
Gwamnan jihar Kadua, Nasir Ahmad El-Rufai, ya sanar da cewa ba zai biya kudin fansa da aka nema ba domin a saki daliban