Rundunar Sojin Libiya ta bayyana cewar ta saki yara kanana da ta kama a gabashin Libiya a lokacinda suke yaki tare da dan tawaye Haftar Khalifa.
Shafin Facebook na Farmakan Bacin Ran Dutse Mai Aman Wuta da Gwamnatin Libiya ke kai wa ya sanar da cewar, an saki wasu daga cikin yara kanana 'yan kasa da shekaru 18 wadanda Haftar Khalifa ya saka a yaki a gabashin kasar.
Sanarwar ba ta bayyana adadin yaran da aka saki ba.
Gwamnatin Libiya ta zargi Haftar da yin amfani da yara a lokacinda yake kai wa Tarabulus hare-hare.
A ranar 4 ga Afrilun 2019 Haftar ya bayar da umarnin fara kai hare-hare don kwace Tarabulus, wanda hakan ya sanya dakarun Libiya fara kai farmakan martani.
A kasar Libiya da ta fada yakin basasa tun shekarar 2011, dakarun gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita na arangama da mayaka magoya bayan dan juyin mulki Haftar Khalifa.